ABNA24 : Jaridar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta buga rahoton cewa wasu majiyoyi a ma’aikatar harkokin wajen Isra’ilan suna nuni cewa biyo bayan tattaunawar da ke gudana akwai yiyuwar Jamhuriyar Nijar ta zamanto kasa ta gaba da za a kulla cikakkiyar alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Jaridar ta ci gaba da cewa ma’aikatar leken asirin Isra’ilan ma ta yi amanna da cewa za a yi nasarar cikin wannan tattaunawa ta sirrin da ake yi don kulla alaka tsakanin Isra’ila da Nijar musamman idan tsohon ministan cikin gida kana kuma dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar PNDS-Tarayya Mohamed Bazoum ya lashe zaben shugaban kasar da za a gudanar a watan Disamban nan mai kamawa.
Jaridar ta jiyo darakatan ma’aikatar leken asirin Isra’ilan Eli Cohen yana cewa zaben shugaban kasa na Nijar mai zuwa yana da muhimmanci wajen ciyar da shirin kulla alaka tsakanin Nijar da Isra’ila.
Har ila yau wasu rahotannin sun ce cikin ‘yan makonnin nan Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammad Bin Salman yana ci gaba da matsin lamba da kuma kwadaitar da jami’an Nijar din wajen su kulla alaka da Isra’ila.
Rahotannin sun ce Nijar za ta zama kasar musulmi ta biyu a yankin da za ta kulla cikakkiyar alaka da Isra’ila bayan kasar Chadi.
Cikin ‘yan watannin nan dai wasu kasashen Larabawa guda uku da suka hada da UAE, Bahrain da Sudan sun cimma yarjejeniyar kulla alaka da Isra’ila biyo bayan matsin lamba da tsoma bakin shugaban Amurka Donald Trump lamarin da ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga al’ummar musulmi na duniya.
342/